Bari muyi karatun a bayyane Gwari-gwari yadda kowa zai fahimta, A dokance Pi Core team suna da nasu ka'idodin kafin su karbi kowace CEX Exchanges, Haka suma Exchanges suna da nasu rules na listing criteria kafin suyi listed na coin/tokens a nasu Exchanges din.
Duk cikin Binance ce mafi girma da buƙatar wadataccen market capitalization zata kai adadin dollar millions $690M a matsayin initial minimum FDV a wajensu kafin suyi listed na coin/tokens bayan listing fees da suke karba na wajen $300k zuwa $500k, na biyun su kuma itace OKX tana buƙatar minimum na $100M zuwa sama.
Pi Core team sun bawa kowace Exchanges daman KYB amma a halin yanzu KYB na Binance ta makalle amma OKX sun tsallake KYB kenan zamu iya Prediction na Pi da adadin minimum na Binance na kusan $700M dake bukata a initial listing na coins, idan muka buga shi da Circulating Supply na Pi guda 6 biliyan, kowane Per coins dai tashi a wajen $0.1 ne zuwa $0.05 🥴
Maximum withdrawal da Pi Core team suka bayar shine iyakar $10,000 daga Pi wallet zuwa CEX Exchanges, akwai whales da yawa da suka mallaki Pi samada 100,000 a Bunburutu ko a mining, Pi Core team zasu sanar dasu farashin kafin hours 1 da listing nashi a kasuwa, wanda zai basu daman lissafa iyakar adadin $10,000 da suke buƙatar Janyewa zuwa CEXs su sayar.
Ni a nawa hasashen, Pi guda 100,000 nafi tsammani a matsayin $10,000 gaskiya 😁 wanda zai kama $0.1 kenan duk Per One $Pi a initial, Idan ma kaƙi sayarwa saboda karancin price da ya baka toh akwai masu sayar da nasu dole kuma tayi massive dump akan gwargwadon adadin masu sayarwa maybe ta dawo $0.05 kamar yadda na fada tun farkon Oktoba-2024.
Duk wannan hasashen ne kawai babu tabbas, tunda muka soma karatun Market Liquidity a $314 Pi ya tashi maybe yanzu kuma zai sauko 📉 Pioneers ayi mini afuwa, Tun Mid- December nake bada shawarar sayarwa Yan Bunburutu. 😔
Pioneers Karatu Yazo karshe, Ubangiji Allah Yasa Mu da Dace 🙏