Har yanzu ana cigaba da amfana daga wasu tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta samar a karkashin ajandar sabunta fata (Renewed Hope) don sauƙaƙawa yan Najeriya a ɓangarori daban-daban, kada mu shagala ba tare da mun amfana ba domin gwamnati ta samar dasu ne domin mu yan Najeriya, mu kuma yaɗa wannan sakon don al'ummar mu su amfana.
Akwai tallafin SUPA Initiative wanda zai bada horo, lasisi da kuma jari ga masu sana'o'in hannu don kara inganta su. Shirin na SUPA Initiative zai shafi mutane Miliyan Goma a faɗin Najeriya cikin shekara 2.
Zaku iya rejista ta yanar gizo-gizo akan adreshin dake ƙasa:
Akwai Tallafin karatun gaba da sakandire na NELFUND, Wani asusu ne da gwamnatin tarayya ta samar don baiwa ɗaliban Najeriya har 260,000 masu ƙaramin ƙarfi damar yin karatun ba tare da tsaiko ba saboda rashin wadata. A halin yanzu, an bada kimanin Naira Biliyan 1.17 ga ɗalibai a sassa daban-daban na Najeriya, har yanzu ana cigaba da nema tare da bayarwa. Za a iya cike form din ta yanar gizo a adreshin dake ƙasa:
A kwai shirin asusun zuba jari na matasa na ƙasa wanda ake kira National Youth Investment Fund (NYIF), wanda aka tsara don samar da damar samun tallafi, lamuni, da kuma saka hannun jari ga matasan Najeriya. An ware wa wannan asusun jimillar kudi har Naira biliyan 110 da aka tanada domin rabawa matasa masu shekaru 18 zuwa 40.
Manufar shirin shine bunkasa sana’o’in hannu, da rage zaman kashe wando a tsakanin matasa, da karfafa hada-hadar tattalin arziki a tsakanin matasan Najeriya.
Ga masu bukatar cike fom, zasu iya ta adreshin yanar-gizo dake ƙasa:
Akwai shirin 3MTT da ake cewa 3 Million Technical Talent (3MTT), shima wani muhimmin bangare na ajandar Renewed Hope na shugaba Bola Tinubu da zai samar da ƙwararrun a ɓangaren fasahar zamani a Najeriya don ƙarfafa tattalin arzikin mu da kuma sanya Najeriya a matsayin kasa mai wadatar ilimin kimiyyar zamani. Akwai darussa da kuma damammaki da yawa tattare da wannan shirin, matasan da ke sha'awar wannan dama zasu iya cikewa a adreshin yanar-gizo dake ƙasa:
Akwai shirin Renewed Hope Cities wanda zai samar da gidaje 100,000 ga yan Najeriya masu matsakaicin karfi. A halin yanzu an soma gudanar da wannan shiri, masu bukata zasu iya bin adreshin yanar-gizo dake ƙasa:
https://renewedhopehomes.fmhud.gov.ng
Akwai shirin Consumer Credit wanda aka samar don don haɓaka damar samun lamuni ga yan Najeriya masu aiki nan da 2030. Tsarin zai inganta kasuwa tare da samar da jari dan habbaka kasuwanci da tattalin arziki.
Masu bukatar kasancewa cikin shirin zasu iya bin wannan adreshin yanar-gizo dake ƙasa:
Wannan duka tsare-tsare ne da aka soma don tabbatar da samun sauƙi ds ingatacciyar rayuwa ga ƴan Najeriya, kuma kamar yadda yake a tsare-tsaren Sabunta Fata (Renewed Hope) na shugaban ƙasa Bola Tinubu, za a sake samar da wasu matakan don cigaba da share hawayen ƴan Najeriya.