YADDA ZAKA ZAMA ƊAN KASUWA A INTANET BA TARE DA BABBAN JARI BA

2025-04-20 09:30:44 - Usman Tech

A yau, intanet ya sauya yadda ake gudanar da rayuwa da kasuwanci. Mutane da dama na samun miliyoyin naira daga ayyuka da dama ta intanet, ba tare da sun kafa manyan ofisoshi ko sun mallaki jari mai yawa ba. Wannan muƙala za ta fayyace hanyoyin da matashi ko duk mai sha'awar kasuwanci zai iya bi don zama ɗan kasuwa a intanet cikin sauƙi da kwarewa ba tare da buƙatar babban jari ba. 


1. Drop Shipping: Kasuwanci ba tare da mallakar kaya ba


Drop shipping wata hanya ce ta siyar da kaya a intanet ba tare da ka siya ko ajiye su ba. Kai dai zaka buɗe shago na intanet (ko ka yi amfani da WhatsApp/Facebook), ka tallata kayayyakin wani, idan kwastoma ya siya, sai kamfanin kayayyakin ya kai masa kai tsaye.


Fa’idodi:

Babu buƙatar ajiya ko jari mai yawa.

Kana iya gudanar da shi daga gida.


Misali:

Zaka iya amfani da shafukan AliExpress, Jumia, ko Konga don siyar da kaya a madadin su, ka karɓi ribarka.


2. Affiliate Marketing: Samun kuɗi daga tallata hajjar wasu


Affiliate marketing na nufin tallata kayayyakin wasu kamfanoni ko masu kasuwanci, idan wani ya siya daga hanyar da ka bayar, zaka samu kaso a matsayin ladan talla.


Shafukan da ke bayar da dama:

Amazon Affiliate

Expertnaire

Jumia Affiliate Program

ClickBank

Dss.


Abunda ake buƙata:


Facebook page, WhatsApp group, ko YouTube channel.

Link ɗin affiliate da zaka dinga yaɗawa.


3. Social Media Influencing: Zama sananne a yanar gizo


Idan kana da mabiya da yawa a shafukan sada zumunta kamar Facebook, TikTok, ko Instagram, zaka iya samun kuɗi ta hanyar tallata samfuran kamfanoni ko shirye-shiryen gwamnati ko ayyuka.


Yadda zaka fara:


Gina abun da ke jan hankali (entertainment, ilimi, barkwanci, ko bayani).


Da zarar ka samu mabiya masu yawa, zaka fara samun sponsorship deals da talla.


4. Digital Services: Ayyukan da zaka iya yi daga gida


Idan kana da ƙwarewa a fannonin zamani, zaka iya sayar da kwarewarka:

Graphic Design

Video Editing

Content Writing

Voice-over & Audio Production

Website Design & Development


Shafukan da zaka yi amfani da su:

Fiverr

Upwork

Freelancer

LinkedIn


5. Koyarwa ta Intanet (Online Tutoring & Courses)


Idan kana da ƙwarewa a wani fanni, zaka iya koyarwa ta intanet ko ka ƙirƙiri kwasa-kwasai (courses) da zaka siyar.


Hanyoyin:

Yin amfani da WhatsApp ko Telegram group don karatu.

Ƙirƙirar eBook ko video course.

Amfani da shafukan kamar Selar, Teachable, ko Thinkific.


6. Blogging/YouTube: Zuba ilimi, da samun kuɗi


Rubuce-rubuce a blog ko samar da faifan bidiyo a YouTube na iya zama hanyar samun kudaden shiga. Idan kana samar da abun da mutane ke bukata, zaka iya samun kudi daga talla (ads), haɗin gwiwa, da sponsorship.


Samun kuɗi a intanet ba sai kana da babban jari ba. Abin da ake buƙata shine fasaha, hazaka, da jajircewa. Tare da wayar hannu da haɗin intanet, zaka iya kafa tushen kasuwancin ka cikin ɗan lokaci. Mu daina ɗaukar intanet a matsayin wurin nishaɗi kawai lokaci ya yi da za mu juya shi zuwa wata babbar kafa ta samun kuɗi da cigaba.


Ka fara da abin da kake da ƙwarewa ko sha’awa a kai, kuma ka dage da gaske. Duk wanda ya ɗora niyya, yana iya samun nasara a duniyar kasuwancin intanet


✍️Isma'il AU

More Posts