Matsalar da yawancin masu amfani da OPAY suke tsoron ta faru shine idan ɓarawo ya sace wayar nasu ko suka rasa wayarsu bayan kuma akwai Mobile App nasu na OPAY da kuɗaɗensu a ciki, to akwai wani tsari na Emergency da OPay suka samar ta yadda zaka iya blocking account ɗin naka..
Koda kuwa hac-king na Opay Account naka akayi, akwai wasu hanyoyi da ake bi ayi Blocking Account ɗin.
Idan ka rasa wayarka kuma kanason kayi blocking ko restricting na account ɗin naka saboda gudun unknown intruders ko scammers su sace maka kuɗaɗe ga yadda zakayi..👇
Ka samu wayar wani abokinka ko ɗan'uwanka ka danna *955#
Sai kayi Selecting wurin da aka rubuta "Manage Account" daganan Sai ka sake Selecting "Restrict Account" daganan kuma sai ka sake Selecting "Stop debit transactions for others".
Daganan zasu baka dama ka rubuta Wallet Number, wato lambar wayar naka da Payment Pin naka which is 4 Digits numbers. Kana gamawa za'a rufe Account ɗin.
Note: Daga Lokacin da kasamu kayi Welcome Back na layinka zaka iya dawo da Account naka ta hanyar da kabi da wannan wayar ta abokin naka.
Kuyi Share Domin Sauran Ƴan Uwa Su Amfana Kamar yadda Kaima ka sani A Yanzu Mungode,
✍️Salisu Abdurrazak