Wani abu da bukusa ni ba dangane da Ai Artificial intelligence

OpenAI wani kamfanin Artificial Intelligence ne da su Elon suka samar don fadada harkokin AI, satin da ya gabata ranar Wednesday suka sake

2023-11-15 14:04:02 - Hassan musa hassan

A tsawon shekarun da aka shafe ana amfani da manhajar Google Search Engine a matsayin wata damar da biliyoyin mutane suke amfani da shi wajen bincike, a wannan karon kuma Elon Musk ya baro wani aikin. OpenAI wani kamfanin Artificial Intelligence ne da su Elon suka samar don fadada harkokin AI, satin da ya gabata ranar Wednesday suka sake manhajarsu ta chatbot mai suna ChatGPT domin testing wacce take amsa tambayoyi duk yadda suke da tsauri. Duk yadda tambaya ta kai ga tsauri ChatGPT zai amsa maka. Satire, riddle, hyperbole, complex questions duka ya sani. Shi ya sa Engr. Ibrahim Auwal ya ce idan aka sake aka bar students da internet connection a exam hall babu wanda zai fita da B, sai dai A's. Idan aka zo assignments kuma kawai copy and paste din questions din za ka yi, kar ka canja komai, shi zai amsa maka tare da steps. To mene ne amfanin bata lokaci kana tambayar wani yaya ake abu kaza... Sannan chatting za ku yi da shi wato chatbot, ya fahimce ka kai ma ka fahimce shi sosai. Ya samu users sama da miliyan daya, amma har yanzu testing ake yi. Yana koyon abu ne ta hanyar amfani da fasahar Machine Learning. Wasu sun fara tsorata da lamarinsa saboda zai iya kawo hármful results bisa ga tambayar da ka yi masa, sai dai a kan wannan batun an shigar da korafe-korafe sosai kuma suna kan improving dinsa. Oga, technology is beyond our expectation!

More Posts