HANYAR DA GRAPHIC DESIGNER ZAIBI WAJEN GANE SUNAN FONT

2024-11-08 14:19:09 - Usman Tech

Duk wani salo na samfuri da zaku ga anyi ma wani rubutu a cikin graphic design to an samu damar yinshi ne daga fonts.


Kamar yadda muka sani ba'ayin gini na gida ko na wani abu sai da block da cement, to haka ma duk wani design da za'ayi sai an mallaki resources wa'danda suke taimakawa sosai a yayin gudanar da aikin mutun, har ya samu yayi shi yadda ake bu'kata.


Fonts suna daga cikin manya-manyan resources da suke da muhimmanci sosai a cikin graphic design, sannan kuma ya zama dole ga dukkanin wani 'dalibin ilimin graphic design da yasansu ciki da bayansu, yasan hanyar samunsu kuma yasan hanyar da zai iya tantancewa da za'kulosu a duk inda ya gansu.


Akwai website-website da dama da ake yin download na fonts daga cikinsu, wasu akwai na kyauta haka kuma wasu akwai wa'danda ake sayarwa, ma'ana sai mutun ya biya ku'di kenan.


Daga cikin website dinda suke taimaka ma duniyar graphic design ta 6angaren kula da fonts akwai:


http://Fontsquirrel.com


Wannan website din suna taimakawa sosai matu'ka domin ba iya font zaka iya download ba a wajensu, har font 'dinda baka san sunanshi ba zaka iya daukar hotonshi kaje cikin website din kayi scanning nashi domin su tantanche maka shi, sannan su baka sunanshi da kuma baka damar yin download nashi idan suna dashi, imma na kyauta ne imma kuma na ku'dine wanda zaka siya.


Idan mutun ya shiga cikin website din daga farko akwai inda zai ga an rubuta Font Identifier, nanne wajen da zasu baka dama kayi scanning na hoton font 'dinda ka dauka.

 

Sau da yawa graphic designers suna samun matsala wajen gudanar aikinsu ta dalilin rashin samun font wanda zaiyi masu daidai da yadda suke bu'kata, wanda hakan yake saka wasu suyi ta shiga website kala-kala suna bincike, wasu kuma sai dai su kira abokanan aikinsu ko malamansu na ilimin graphic design.


Daga cikin website dinda ake samun fonts bila-adadin, har a samu damar yin download nasu akwai:


Fontmeme.com

Freefonts.com

Fontfabric.com

Fontpair.com

Font.google.com


A wasu lokutan idan na kasance free bana komai nakan ziyarci irin wa'dannan website-website 'din domin samo fonts, in adanasu kawai domin nasan suna da amfani a wajena.


Idan dai har ka kasance graphic designer ko kana da sha'awar kasancewa graphic designer to ina mai baka shawara da ka maida hankali sosai a fannin ilimin sanin fonts, domin suna taimakawa matu'ka, dan a wasu lokutan ma zaka iya samun aikin da sune ka'dai zakayi amfani dasu a matsayin resources naka har ka kammala aikin.


Allah Ya taimaka. 


✍🏼 Usman Fasaha Tv

More Posts