AMFANIN BLUE BADGE NA FACEBOOK

Na fuskanci akwai mutane da yawa da basu fuskanci amfanin blue badge da Facebook ta yi monetizing ba. Wasu har rantsuwa suke ba shi da amfani. Eh, zai iya yiwuwa ba shi da amfani a gare su amma hakan ba ya na nufin ba shi da amfani ba ko kuma babu waɗanda zai yiwa amfanin.

2023-11-09 15:15:25 - Hassan musa hassan

Daga cikin amfanin sa akwai;

1. Authenticity: A kafafen sada zumunta da ma yanar gizo, akwai abinda ake kira da "authenticity" wanda ke nuni da cewa kai da ka ke da account kai ne haƙiƙanin mammallakin account ɗin ba wani ba. Wannan abu na cire shakku a zukatan mutane, followers da kuma masu siyan hajar ka idan kai mai gudanar da kasuwanci ne a waɗannan kafafen. Wannan blue badge ɗin ya na kawar da shakku akan waye kai saboda hanyoyin da ake bi wajen samun sa.

2. Improved Visibility: Wannan na nufin wanda ya mallaki wannan verification badge ɗin, mutane za su fi ganin abubuwan da ka ke yi a wannan kafa ta Facebook. An tabbatar cewa wanda ya ke da wannan blue badge ɗin, post ɗin sa ya fi sauƙin yawo da isa a wurin followers a kafar Facebook. Kun ga kuwa, ga masu sana'a ko kuma influencers da ma sauran waɗanda ke promoting wasu causes masu ma'ana, wannan abu zai amfane su.

4. Tabbatarwa da mutane irin muhimmancin da ka bawa online presence. Kamar yadda masana suke faɗa, gina online presence mai kyau na amfanar mutane sosai a harkokin sana'o'in su da ayyukan su da ma wajen neman aikin ko wasu damarmakin na daban. Kamar yadda na ga Turawa da wasu mutane a wasu ƙasashen ke ɗaukar wannan batun da muhimmanci, na fahimci cewa akwai fa'ida. Saboda wannan cigaba ne a online presence kuma ba dainawa Zukerberg zai yi ba.

5. Ra'ayi. Ba kowane ne zai buƙaci wannan blue badge ɗin ba kamar yadda muka sani. A kowane gari akwai wasu wurare da sai mutum ya biya kuɗi sannan za a barshi ya shiga, haka wannan sabgar ba ta kowa bace kuma ba dole bane. Sabga ce ta wanda ya ke da ra'ayi. Duk inda aka ba ka zaɓi kuwa, an girmama ka.

More Posts