ANDROIDAPPLICATIONSTECHNOLOGY

YADDA ZAKA SAMU FIYE DA 1000 VIEWS A WHATSAPP STATUS

YADDA ZAKA SAMU FIYE DA 1000 VIEWS A WHATSAPP STATUS

Wannan wata hanya ce ta samun views masu yawa a WhatsApp status! wadda za’a iya amfani da hanyar wajan tallata kasuwanci, kokuma isar da sako ga masu kallon status din cikin kankanin lokaci.

Kamar yadda kowa ya sani, kamfanin WhatsApp suna da doka akan babu wanda zai iya ganin status din ka, dole sai wanda yake da lambar ka, kaima kake da tashi lambar!

Hakan ke sa da yawan mutane suna da masu yi musu magana a WhatsApp sosai, saidai sakamakon ajiye lambar kowa (SAVING) ya zama babban aiki, zai iya cin lokaci sosai fiye da yadda ake tunani.

Akwai hanyoyi ka ƙa’idodi da zaka bi wajan ganin cewa duk wanda yayi saving lambar ba, yana kallon status din ka, ba tare da kayi saving tashi lambar ba da kanka!

Saidai kafin ka samu wadanda za su yi maka magana a WhatsApp din, har ma suyi saving lambar ka, hakan zai iya zama abu mai matukar wahala sosai, amma zaka iya bin wadannan hanyoyin:

 • Ka samu wani guri a Social Media, kamar facebook page, ko YouTube channel, ka sanya lambar ka, kace ayi maka magana ta lambar
 • Ka sanya kyauta, kokuma wani abu na jan hankali ga wadanda suke kallon status din ka!
 • Zaka iya tunanin duk wasu hanyoyi da zaka bi wajan janyo mutane gare ka, ta WhatsApp.

Bayan ka tabbatar kana da mutane da yawa da suka ajiye lambar ka a wayar su, abu na gaba shine kaima ka ajiye nasu lambobin a wayar ka

Saidai kuma hakan zai iya daukar dogon lokaci, kokuma ya gajiyar da kai!

hanya mafi sauki da zaka bi shine, kayi amfani da computer wajan saving din gaba daya lambobin da suka yi maka magana a WhatsApp wadanda baka yi saving ba.

Hanyoyin sune kamar haka:

 • Zaka fara da danna wannan link din a cikin computer, ga link din
https://chrome.google.com/webstore/detail/ikontacts-for-whatsapp/pgmeblokoongfgbidlocklmdhhbjknpc
 • Sai ka duba daga gefe ka danna alamar ADD TO CHROME kamar haka
 • Bayan kayi add, sai ka danna alamar extention dake sama, sannan ka danna alamar PIN 📌 kamar haka:
 • Bayan kayi PIN, sai kuma ka bude sabon tab kayi login din WhatsApp din da yake da lambobin, wannan shine link din da zaka bude a sabon tab:

web.whatsapp.com

 • Sannan ka danna alamar iKontacts da kayi PIN 📌 zai fito kamar haka
 • Sai ka danna alamar EXPORT TO TEXT FILE
 • Nan take zai duba duk lambobin da baka yi saving ba, yayi maka download din su a matsayin TEXT FILE (.txt)
 • Sai kayi saving file din na .text a wayar ka.
 • Sannan ka dakko wannan application din a wayar ka, ta wannan link din:
https://play.google.com/store/apps/details?id=exportphone.silverlinesoftwares.com.exportphone
 • Kana dakko application din, sai ka bude shi, sannan ka saita shi kamar haka
 1. Da farko ka fara shiga SELECT FILE ka dakko wannan file din da kayi download daga computer
 2. Sai ka zabi EXPORT PHONE VCF
 3. Sannan ka rubuta sunan da kake son lambobin su kasance da shi
 4. Sai ka zabi alamar COMMA ,
 5. Sannan ka danna alamar EXPORT

zai ajiye maka su a cikin wayar ka, a folder mai suna EXPORTCONTACT da format din .VCF

 • Kaitsaye sai ka shiga file manager na wayar ka, ka nemo file din ka danna shi
 • Zai baka damar ka zabi Application, sai ka bude shi da Application din CONTACTS kamar haka
 • Sannan ka zabi Gmail din da zaka dora lambobin a kai.

SHIKENAN

zai yi maka saving wadannan lambobi da sunan da kasa, tare da yi musu lambobin, misali, tun daga 0001 har zuwa adadin lambobin.

kana shiga WhatsApp kayi status, duk wanda yayi saving lambar ka cikin su, zai ga status din!

KAMAR HAKA ☝️

Domin samun ƙarin bayani dangane da yadda ake amfani da shi, kokuma kallon yadda ake yin shi a bidiyo, kalli Wannan bidiyon na ƙasa

MUN GODE

Abdulfatah

CEO FOUNDER OF AREWA DAILY TRICKS I'm a real YouTuber | Blogger | Programmer | Web Designer | App Developer | Crypto Trader | Cyber Army | Graphic Designer | --But sometimes I'm 🎭ANONYMOUS🎭

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button