Uncategorized

YADDA ZAKA YI REGISTAR KATIN ZABE TA CIKIN WAYAR KA

DOMIN YIN PERSONAL VOTER’S CARD (PVC)

Ta cikin wayar ka, akwai abubuwa da yawa da zaka lura da su, kamar yadda muka sani, PVC kokuma katin zabe, shine katin da gwamnati ke badawa wanda ake amfani dashi wajen zabar shuwagabanni a kasar Najeriya.

Duk wani dan kasar Najeriya da ya wuce shekara 18 yana da damar yin katin zabe, saidai kamar yadda aka saba, ana zuwa zuwa ofishin INEC ne domin yin katin!

A wannan darasin zan nuna mana yadda kowa zai yi register katin zabe ta cikin wayar shi, matukar ya haura Shekarun da ake bukata.

Ba iya register kadai zaka iya yi da wayar ka ba:

 • Zaka iya canza bayanan katin ka, idan kana da shi, kana so ka canza suna ko ranar haihuwa.
 • Zaka iya canza Polling Unit (wajan yin zaɓe)
 • Zaka iya duba bayanan katin ka
 • Zaka iya tura bukatar buga sabon kati, idan ka rasa tsohon katin ka, kokuma ya lalace.
 • Zaka iya duba matakin rajista, misali: idan ka yi register kana so ka san a matakin da registar take.
 • Zaka iya duba ofishin INEC mafi kusa da kai wanda zaka je ka karbi katin ka (idan kayi sabon kati, kokuma ka tura bukatar buga sabon kati)

Banda wannan ma, akwai abubuwa da yawa da ake yi a website din,

Domin duba bayanan katin ka, canzawa, ko yin Sabuwar rajista, shiga wannan link din dake ƙasa

https://cvr.inecnigeria.org/Public/getStarted

Sanna ka duba daga sama zaka ga wajan da aka sa, sign in / register kamar haka

Sai ka danna wajan domin kayi login, kokuma ka kirkiri account da website din,kana gamawa zai bude maka cikin website din kamar haka

Zaka ga zabubbuka da yawa, sai zabi wanda kake da ra’ayi, akwai wajan yin

 • Register
 • Duba bayanai
 • Canza gurin zabe
 • Gyara bayanai
 • Karbar katin PVC
 • Tura bukatar buga sabon kati

Idan kana so kayi sabuwar register ne, za su bukaci bayanan ka da yawa, kamar dai yadda za’a bukata idan kaje ofishin INEC din, sai ka natsu, ka cike komai daidai yadda ya kamata

Kasancewar ana bukatar hoton zanen hannun ka (FINGER PRINT) domin kammala register, za su bukaci ka zabi rana da lokaci da kuma ofishin da zaka je a dauki hoton zanen hannun naka, ka cike komai yadda ya kamata domin gudun matsala!

Idan kuwa ka bukaci canza bayanai, ko transfer da sauran su, za su bukaci ka sanya cikakkun bayanan katin ka, a wasu lokutan ma wajan canza suna ko shekarar haihuwa, za su bukaci takardar shaidar kotu, kokuma jarida.

Domin karin bayani akan yadda zaka yi hakan, ka kalli Wannan bidiyon na ƙasa

MUN GODE 🙏

Abdulfatah

CEO FOUNDER OF AREWA DAILY TRICKS I'm a real YouTuber | Blogger | Programmer | Web Designer | App Developer | Crypto Trader | Cyber Army | Graphic Designer | --But sometimes I'm 🎭ANONYMOUS🎭

4 Comments

 1. Mun Gode sosai Allah ya Saka da Mafificin Alkhairi, but please ka koya mana yadda Zamu Bude Blog namu as good as urs🙏🙏

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button