Uncategorized

HOW TO GET PLASTIC NATIONAL ID CARD FOR FREE

YADDA ZAKA SAMU PLASTIC NATIONAL ID CARD TA CIKIN WAYAR KA KYAUTA

Domin samun katin dan kasa, (National ID card) na plastic, wanda hukumar NIMC ke bayar wa, ta cikin wayar ka, Akwai matakai da zaka bi kamar haka 👇

  1. Ka sauke Manhajar NIMC na asali daga playstore ko App Store ta hanyar searching, ko kuma ka sauke NIMC PRO wanda zai baka damar ɗaukar screenshot a wayar Android ta NAN WAJAN
  2. Bayan ka sauke Application din, sai ka shiga, ka sanya lambar ka ta NIN
  3. Za su tura OTP a lambar, sai kayi amfani da shi wajan wucewa mataki na gaba
  4. Sai ka sanya PIN guda 6 wadanda kake da ra’ayi!

Kaitsaye Application din zai bude maka, zai nuno maka HOME na Application din!

ABIN LURA: Akwai plastic national ID card kala uku a ciki wanda zaka iya printing a hannu! Saidai guda biyu daga ciki na kudi ne, daya kuma na kyauta!

Ba za su baka damar da zaka dauki screenshot na katin kyauta ba (STANDARD ID), dole saidai ka biya kudi ka sauke PDF na PREMIUM ID Wanda ake siya akan farashin ₦1,200

Domin samun Damar ɗaukar screenshot na katin kyauta (STANDARD ID), kayi amfani da Application din NIMC PRO ka dauki screenshot!

Kaitsaye idan da NIMC PRO kake amfani, daga home na Application din zaka iya danna alamar SHOW MY ID kamar haka 👇

Zai nuna maka Katin ka na NATIONAL ID CARD, Kaitsaye sai ka dauki screenshot, ka kai wajan masu SHAGON CAFE su yi maka printing din shi!

Ko kuma ka bi wadannan matakan ka biya kudi domin siyan PREMIUM ID, matakan sune kamar haka:

  • Ka danna alamar PRINT NIN SLIP daga home na Application din, kamar yadda ya nuni a nan:
  • Zai cike maka bayan da zaka yi login da kanshi, Kaitsaye sai ka danna alamar login
  • Sai ka zabi kalar ID CARD din da kake so, suna da ID CARD guda biyu, zaka gan su daga gefe kamar haka
  • Kana shiga wanda kake so, zaka ga farashin shi, sai ka danna alamar PAY WITH REMITA
  • Kaitsaye zai kaika indazaka biya wadannan kudin, zaka iya biya da Katin ATM ko da Banki
  • Bayan ka biya successfully ✅, zai wuce da kai gurin da zaka dauko PDF na ID CARD din ka, sai ka danna alamar download domin dakkowa!

ABIN LURA: bayan ka biya kudin, kar ka fita daga wajan har sai ka tabbatar ka dakko PDF na ID card din, domin idan ka fita, sai ka sake biya sannan za su sake baka damar shiga wajan!

DOMIN FIDDAWA: zaka tura wa masu shagon INTERNET CAFE pdf din, za su yi maka printing din shi su baka, kudin printing bai wuce ₦300 zuwa ₦500 duk kayi daya!

💥SHIKENAN BOOM 💥

Abdulfatah

CEO FOUNDER OF AREWA DAILY TRICKS I'm a real YouTuber | Blogger | Programmer | Web Designer | App Developer | Crypto Trader | Cyber Army | Graphic Designer | --But sometimes I'm 🎭ANONYMOUS🎭

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button