ANDROIDAPPLICATIONSTECHNOLOGY

HOW TO TRACK LOST ANDROID

YADDA AKE GANO WAYAR DA AKA SACE (TRACKING)

Akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan gano wayar da aka sace, saidai ba kowa ne zai iya amfani da kowacce hanya ba, misali, ana amfani da IMEI number domin gano inda waya take, amma sai hukuma kaɗai ke da damar hakan 😢

A duk lokacin da aka sace waya, babban abin da ake yi shine a kira wayar domin a ji ko tana a kunne ko kuma an kashe ta, saidai mafi yawa ana jin wayar a kashe ne, kuma kamar yadda aka saba gani, duk wayar da aka kashe, babu wanda zai iya gano inda take koda kuwa hukuma ne!

Idan ka biyo ni a cikin wannan rubutun, xan maka cikakken bayanin yadda zaka gano wayar da aka sace, koda kuwa an kashe wannan wayar, ko kuma an sa ta a Airplane mode✈️ ba tare da kaje wajan hukuma ba

Amma da farko ya kamata ka sani, dole ne sai ka saita abubuwan da xan nuna maka a yanxu kafin a sace wayar, idan baka saita su ba har aka sace wayar, to wannan hanyar ba zata yi aiki ba, saidai ka nemi wata hanyar daban

Kana bukatar sauke Application mai suna hammer security a kan wayar ka domin yin wannan aikin, ga bayanai kaɗan dangane da abin da hammer security zai iya yi maka a kan wayar idan ka saita shi

ABUBUWAN DA ZAKA IYA YI

 • Za kayi tracking din waya ko da an kashe ta
 • Za kayi tracking din waya ko da an sa ta a Airplane mode ✈️
 • Za ka iya dauko hoton wanda wayar ke hannun shi ta wata wayar
 • Za ka iya sauraren abinda ke faruwa a inda wayar take
 • Za ka iya ganin bidiyon abin da ke faruwa a inda wayar take
 • Za ka iya sanya wayar tayi ƙara (Alarm) daga cikin wata wayar
 • Za ka iya kashe wayar, ko kunna ta, ta cikin wata wayar

Wadannan wasu ne daga cikin ayyukan hammer security idan aka saita shi a waya, za ka iya bincike domin samun ƙarin bayani dangane da yadda hammer security yake aiki!

YADDA ZAKA SAITA SHI

Akwai madannin da aka rubuta download now a karshen wannan rubutun, ka danna shi domin dakko Application din Hammer Security, idan ka dakko shi sai ka bude shi kamr haka

Sai ka danna alamar settings, inda Arrow ya nuna, zai baka fuska kamar haka

Za ka fara da shiga wajan create account, kasa e-mail din ka, da password 🔑 domin ka ƙirƙiri account, idan ka gama kuma sai ka shiga wajan subscription za kaga ya nuna maka 0.6 days!

ME SUBSCRIPTION KE NUFI?

Application din suna da tsarin cewa sai ka biya kudi ko kuma ka kalli talla domin ƙara yawan kwanakin da Application din zai yi a kan wayar ka yana aiki, dan haka da zarar lokacin da suka baka ya ƙare to Application din zai daina aiki a kan wayar ka

HANYAR ƘARA LOKACI

Domin ƙara lokacin da application zai yi aiki a kan wayar ka kyauta, ka shiga wajan da aka sa redeem code kasa wannan code din HN2VP Kayi submit, za su ƙara maka kwana talatin a kan lokacin da kake da shi, sannan kuma za ka iya shiga wajan watch ads ka kalli talla, duk talla daya da ka kalla za su ƙara maka kwana biyu a cikin lokacin da kake da shi, za kuma ka iya shiga wajan invite code ka dauki code din ka, duk wanda ya bude application din a wayar shi yayi register, ya sa code din ka a wajan redeem code za su baka kwana talatin, shi ma su bashi kwanan talatin, idan haka zai maka wahala, za ka iya amfani da App cloner, App cloner ++, multi space, ko multiple account domin kayi fake referral ka ƙara lokaci kamar shekara daya ko biyu! Idan baka san yadda ake fake referral ba, ka danna NAN WAJAN

YADDA AKE SAITA SHI

Bayan kayi login, kuma ka tabbatar kana da isasshen lokaci a wajan subscription, sai ka dawo home ka bude wasu daga cikin abubuwan da ke wajan kamar haka

Application din zai bukaci permissions masu yawa a lokacin da kake bude su, dan haka ka tabbatar duk wani permissions da ya bukata ka bashi, duk abin da ake so a bude ka bude, hakan ne zai sa yayi maka aiki ba tare da wata matsala ba, idan kuwa baka bashi wasu permissions din ba, to za’a iya samun matsala ta wasu wuraren!

FAKE SHUTDOWN

A lokacin da ɓarawon ya kashe wayar ka, fake shutdown zai fara aiki, aikin shi shine zai nuna kamar wayar ta mutu, amma kuma tana nan a kunne, saidai ba zata kawo haske ba, ba zata yi ƙara ba, ba zata yi duk wani aiki da za’a iya gane tana a kunne ba! Saidai a ɓoye zai cigaba da tura sako zuwa emergency contact,

Akwai hanyoyi uku da za ka iya fidda wayar ka daga fake shutdown!

 • Ka sanya wayar caji
 • Ka tura sakon HS1 FS OFF zuwa cikin wayar
 • Kayi login a website din su, ka rufe fake shutdown

wannan yana da matukar amfani, ka kula da shi sosai

EMERGENCY CONTACT

Akwai bukatar ka sanya emergency contact ( lambar waya) wadda za’a rinka turawa saƙo lokaci lokaci dangane da halin da wayar take ciki, kuma a duk lokacin da ka bukaci a nuna maka inda wayar take, to ta cikin emergency contact za a Turo maka da location din ta, dan haka ka tabbatar lambar da kasa ba ita ce ke cikin wayar ba, domin idan ita ce ke cikin wayar to kamar baka sa bane, za ka iya sa lambar abokin ka, ko wani wanda kake da damar karɓar wayar shi a lokacin da ka rasa taka! za ka iya sanya lambobi da yawa, ba dole sai daya ba

FAKE AIRPLANE MODE ✈️

Akwai Airplane mode da hammer security yake da shi na ƙarya, za ka iya sanya shi ta wajan notifications na wayar ka, yana bada damar da idan aka sanya wayar taka a Airplane mode, network ba zai dauke ba, za ta cigaba da aiki normal, amma zai nuna kamar tana Airplane mode ne!

LOW BATTERY SMS

Idan cajin wayar ka ya koma 5% za ta tura sako zuwa emergency contact cewa wayar ta kusa ɗaukewa, dan haka idan kana so ka gano inda take, to ka hanzarta!

INTRUDER SELFIE

Idan aka gwada cire securityn wayar ka har sau uku ba daidai ba, kaitsaye wayar za ta dauki hoton wanda ya gwada cirewar da camerar SELFIE, ta tura shi zuwa emergency contact!

CAR COLLISION DETECTOR

Yana amfani da sensor da kuma speedometer domin ya gane hatsarin mota, idan aka yi hatsari da mota ko mashin, ko wani abin hawa, wayar za ta tura sako dauke da location din inda abin ya faru zuwa emergency contact (Allah ya kiyaye)

EMERGENCY MODE

A duk lokacin da wani abu mara kyau ya faru ( kamar fake shutdown, ko Airplane mode ) wayar za ta shiga emergency mode, Dan haka idan wayar na tare da kai, yana da kyau a koda yake ka kashe emergency mode, domin shi ke nuna cewa wayar na tare da kai!

YADDA ZAKA GANO WAYAR IDAN AN SACE TA

Akwai hanyoyi guda biyu, ONLINE TRACK da kuma OFFLINE TRACK Kowanne Yana aiki sosai wajan gano wayar ka!

OFFLINE TRACK

Yana baka damar da za ka gano inda wayar ka take ba tare da akwai DATA a cikin wayar da aka sace, ko wayar da za’a gano da ita din ba, yana amfani da SMS COMMAND ne wajan control din wayar, misali, da ka samu waya a kusa da kai, sai ka tura sako a layin dake cikin wayar da aka sace din ta wajan messages, yanayin sakon da ka tura, yanayi aikin da wayar za tayi, misali, za ka iya tura

 • HS1 TRACK domin a tura da location (inda wayar take) cikin emergency contact
 • HS1 ALARM wannan sakon na shiga, wayar za fara ƙara ne kawai
 • HS1 STOP ana amfani da shi wajan kashe emergency mode
 • HS1 FS ON Yana aiki wajan kashe wayar (fake shutdown)
 • HS1 FS OFF Yana aiki wajan kunna wayar
 • HS1 MESSAGE Domin rubuta sako a fuskar wayar

Duk wanda ka tura, za’a tura sako tabbacin zuwa cikin emergency contact

ONLINE TRACK

Yana aiki ne ta hanyar data, kai tsaye za ka samu wata wayar ka shiga website din su na www.hammer-security.ca/en/signin/ ka sa email da password irin wanda ka sa a lokacin da kayi registar hammer din, daga nan zai nuna maka commands, sai ka zaɓi wanda kake so kamar haka

Duk wanda ka danna, zai maka aikin a nan take, saidai dole ne ya zama cewa akwai Data sannan kuma a buɗe take a cikin duka wayoyin!

ABIN LURA ⚠️

 • Dole sai akwai DATA kuma tana kunne a kowacce waya, domin yin Online Track
 • Dole sai akwai isasshen katin kira (Airtime) a cikin kowacce waya, domin yin Offline Track

SHAWARA ✌️

 • Barin data a kunne koda yaushe na da matuƙar amfani ga wayar ka, saidai hakan yana shanye cajin waya da wuri
 • Ka rinƙa duba hammer security lokaci zuwa lokaci domin tabbatar wa yana aiki yadda ya kamata!
 • Isasshen katin kira a wayar ka yana da matuƙar amfani nesa ba kusa ba, ka kula da shi sosai

GARGADI ⚠️

Ya zama wajibi ka fahimci yadda tsarin yake sannan ka saita komai daidai idan akan so yayi maka aiki, Dole sai Hammer Security yana aiki a cikin wayar da aka sace ne za’a iya gano ta da shi,

Babu tabbacin zaka gano wayar ka ko da hammer security Yana aiki a kanta, saidai ka yi abin da zaka iya yi, idan gano ta ya gagara to saidai ka tuntuɓi hukuma su yi maka nasu aikin

ABUBUWAN DA ZA KA BUKATA

Danna wannan madannin domin dakko manhajar Hammer security daga playstore

Ka danna wannan madannin dake ƙasa domin shiga website din Hammer Security kayi login

DOMIN GANIN YADDA AKE SAITAWA A BIDIYO, KA KALLI WANNAN BIDIYON NA ƘASA 👇

MUN GODE 🙏

Abdulfatah

CEO FOUNDER OF AREWA DAILY TRICKS I'm a real YouTuber | Blogger | Programmer | Web Designer | App Developer | Crypto Trader | Cyber Army | Graphic Designer | --But sometimes I'm 🎭ANONYMOUS🎭

Related Articles

10 Comments

 1. Assalamu Alaykum
  You are doing a good job and his helping, but the process of activation is not easy,
  Kasan badukkammu mukaje makaranta sosai ba dazaku iya rege process din wallahi da abun yayi kiyau.

 2. You’re really help people, because you have good intentions on us, the things you are doing is good, but you have to simplify the process because its too long. There are some of us we could not follow the process complete without problem, then eventually if you do not follow correctly it will be in include. At end you will miss the application at all. Pls rehelp us again.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button