APPLICATIONSTECHNOLOGY

HOW TO BYPASS OTP IN NIMC APP

YADDA ZAKA TSALLAKE MATAKIN OTP VERIFICATION A MANHAJAR NIMC

  • O : one
  • T : time
  • P : password

Wani mataki ne na tsaro da a kanyi amfani da shi a wasu wurare da dama domin tabbatar da cewa mai abu ne da kanshi yake shiga, ana amfani da OTP domin ƙara tabbatar da tsaro da kuma ingancin account, wanda ake tura lambobi a layi ko email a bukaci a sanya su a daidai lokacin, kowanne OTP na amfani sau daya ne kawai, yana da ƙayadadden lokacin da zai yi expire

NIMC APP

Application ne na gwamnatin Najeriya ta ɓangaren Katin ɗan ƙasa, wanda zai baka damar da za ka ajiye katin ka na National ID card a cikin wayar ka, a wasu lokuta ma har kayi printing din shi!!

Saidai su kan bukaci su tura maka CODE a layin da aka yi rajistar katin da shi domin shiga da fara amfani da Application din, suna yin hakan ne domin su tabbatar da cewa mai layin ne da kanshi yake ƙoƙarin shiga Application din!

Amma kuma mafi yawa akan samu matsaloli dangane da hakan, wasu lambar da aka bude NIN din da ita ta ɓata, wasu kuma basa tare da lambar, wasu kuma an samu kuskure wajan rubuta lambar,

Kasancewar a lokacin da kake kokarin shiga Application din NIMC za su tura OTP a ita lambar, hakan ke sa wadanda suke da matsaloli dangane da lambar waya dole su yi hakuri da shiga..

Amma yanxu zan yi maka bayanin yadda zaka tsallake matakin OTP verification a application din NIMC, hakan na nufin, za ka iya shiga Application din ko da baka da lambar da aka bude katin da ita!

GARGAƊI

Za mu nuna wannan hanyar ne domin ilmantarwa, da kuma samun sauki ga wadanda suke da matsaloli dangane da hakan, dan haka duk wanda yayi amfani da wannan hanyar wajan bankaɗo sirrikan mutane, ba da izinin mu ba…

YADDA ZA KAYI

Ka dakko manhajar NIMC na ainihi daga playstore ta hanyar danna NAN WAJAN kai tsaye, ko kuma ka dakko NIMC PRO wanda za ka iya daukar screenshot ta hanyar danna madannin da ke ƙasa

Bayan ka dakko shi, sai ka bude ka sanya lambar NIN din da kake son ganin bayanan ta, daga nan za su tura OTP a lambar da aka bude NIN din da ita, kamar haka

Idan baka da lambar da aka tura OTP din cikin ta, sai ka samu layi mafi kusa da kai ka danna *346*2*NIN# Ka danna alamar kira📞 misali *346*2*22334455667# (za ka sanya lambar NIN din da ka sanya a cikin application din ne)

Ka tabbatar akwai katin ₦20 ko fiye da haka a layin da ka danna lambobin! Idan kayi komai daidai to nan take zaka ga User ID da OTP na wannan NIN din sun bayyana, sai kayi amfani da OTP din a cikin Application din

Kana sanya wa zai wuce, zai kai ka inda za ka sa password 🔑 sai ka zaɓi lambobi guda shida ka sa, ka sake maimaita su, shikenan zai wuce successfully ✅

ABIN LURA

Dole sai kayi requesting OTP ta cikin Application din, sannan ka danna lambobin, sannan kuma ka tabbatar baka dauki dogon lokaci tsakanin requesting na OTP din da danna lambobin ba, domin yin hakan zai iya baka matsala 🔴

MUN GODE 🙏

Abdulfatah

CEO FOUNDER OF AREWA DAILY TRICKS I'm a real YouTuber | Blogger | Programmer | Web Designer | App Developer | Crypto Trader | Cyber Army | Graphic Designer | --But sometimes I'm 🎭ANONYMOUS🎭

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button