APPLICATIONS

VMOS PRO VIRTUAL MACHINE

MENENE VMOS PRO?

VMOS software ce ta Application wacce ta dogara akan Injin Virtual (VM).
Ana iya sauke VMOS ta hanyar Application a kan linux ko wayar Android

VM zai baka damar shiga da amfani da wayar android ta cikin APP.
Bugu da ƙari, VMOS na cin gashin kanshi, ba tare da amfani da bayanan wayar ka ba. (Android cikin Android).

Virtual Android yana ba da damar aiki biyu a lokaci guda akan wayar Android.

VMOS PRO-Virtual Android, gaba ɗaya mai zaman kansa ne daga ainihin tsarin wayar ka. A cikin Virtual Android, duk wasu files ko saite-saite da za kuyi masu haɗari ba za su iya lalata tsarin wayar ku na ainihi ba, kuma VMOS Pro yana tabbatar da cewa duk manhajojin da kuka ajiye a cikin sa ba za su iya samun bayanan sirri na ainihin wayar ku ba.

Don haka, za ku iya sanya duk wata manhaja ta sirri, ko bayan da ke da hadari a cikin VMOS domin tantancewa, a maimakon ku dora su akan wayar ku ta ainihi.

[Wayar Android Kyauta ta Dindindin]


VMOS Pro zai iya installing din duk wani application akan kowacce waya ta Android ba tare da wata matsala ba, don haka duk wani application ko game da ya gagari wayar ku, za ku iya installing din shi a kan VMOS PRO yayi aiki lafiyalau batare da wata matsala ba.

Da VMOS PRO za ku iya amfani da kowanne application ta hanyar window [kamar yadda ake yi a computer] hakan yana nufin za ka iya yin ayyuka fiye da daya a lokaci guda da wayar android ta hanyar amfani da VMOS PRO. misali ka bude facebook, whatsapp, da instagram a tare kayi chatting.

[PRIVACY POLICY]

Wayar virtual machine ba ta da damar ganin wasu bayanai na ainihin wayar ka, don haka za ka iya installing din duk wani application da baka yarda dashi ba akan virtual machine domin ka gwada shi, kokuma ka ajiye duk wasu bayanai da baka aminta dasu ba domin gudun matsala

domin samun VMOS PRO APPLICATION, Kaitsaye danna alamar download da ke kasa

Abdulfatah

CEO FOUNDER OF AREWA DAILY TRICKS I'm a real YouTuber | Blogger | Programmer | Web Designer | App Developer | Crypto Trader | Cyber Army | Graphic Designer | --But sometimes I'm 🎭ANONYMOUS🎭

Related Articles

4 Comments

  1. Oga muna gdy allah yabiyaka ysaka da alkairi ameen wai oga ni wayata S5 Ce version9 zaniya amfani da wannan kokuma kafada min wane zanyi amfani DA shi
    Na gd🙏🙏🤲🤲

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button