APPLICATIONS

VIRTUAL ANDROID FOR FREE TO HAVE A SECOND PHONE

Gina Sabuwar wayar Android ta biyu da zaka iya amfani da ita ta cikin wayar ka!

Virtual Android waya ce mai zaman kanta domin wayar ka ta Android. Za ka ninka amfanin da kake da wayar ka ta hanyar amfani da wata wayar a cikin wayar ka su rinka yin aiki tare – zaka bude account da yawa sannan ka tsare sirrika ka.

Virtual Android yana ƙirƙirar part na daban akan wayar Android, yana aiki a matsayin wata wayar ta daban. Kamar dai amfani da wayoyi daban-daban guda biyu ne! Lokacin amfani da Virtual Android, zaku iya canzawa tsakanin wayar ku ta ainihi, da kuma wayar ku ta virtual phone ta hanyar da taɓawa ɗaya, za ku samu damar bude accounts da yawa a ciki. Za ku iya amfani da kowanne Applications ta hanyar window (kamar yadda ake yinsa computer), kuyi amfani da Applications masu yawa a lokaci daya.

【FREE NE, KUMA SIMPLE NE】

Kamar dai ku siya wata wayar daban ne, ma’ana zaku iya samun WhatsApp dual WhatsApp, Sharechat, Snapchat, FreeFire ,ChipperCash, Pampas, Opay, da sauran wasu apps da yawa wadanda baku da damar bude guda biyu a waya daya. Za ku kirkiri accounts da yawa, sannan kowanne yayi aiki a lokacin da kuke so!!!

【Ku mori daɗin Applications da yawa akan layi lokaci ɗaya】
Games da Apps ana cloned dinsu ne bayan da zarar kun shiga da su cikin Virtual Android, wanda ke nufin cewa zaku iya amfani da account da yawa a lokaci guda akan waya ɗaya ta hanyar tsarin mu mai sauri.

ABIN DA YA KAMATA KU SANI:

  • Wanne adadin storage virtual android ke bukata?

Virtual Android yana gudanar da ayyukan sabuwar wayar Android V7, don haka akwai bukatar yayi downloading na DATA kimanin 600MB domin ya shigo wayar ku, sannan kuma yana buƙatar kusan 2.5GB FREE STORAGE Ko fiye da haka akan wayar ku domin ya fara aiki. Zai iya bukatar ƙarin SPACE idan kuka ajiye abubuwa da yawa a ciki, ko kuma kukayi ayyuka masu cin MEMORY

  • Ko mutum biyu za su iya amfani da virtual Android Daya?

Kowanne virtual Android akwai bukatar ya zauna a cikin waya daya ne, dan haka kowa sai ya nemi nashi ya sa a wayar shi.

  • Me za ku yi idan kuka sami matsala wajan downloading?

Virtual Android yayi depending ne da GOOGLE’S AAB servers domin downloading din bayanan wayar! Idan downloading ya makale to ka sake gwadawa daga farko, idan duk da haka yana baka matsala Sai kayi updating din google play services, idan matsalar ta cigaba to ka goge shi ka sake sabon installing, sannan ka tabbatar kana da isasshen Storage a lokacin da za ka fara sabon downloading na DATAs din!!!

  • Me za kayi idan Virtual Android ya ki shiguwa??

A mafi yawan lokuta, irin haka na faruwa ne idan aka samu tangarɗa wajan wasu files da suka lalace a virtual Android din, Dan haka ka tabbatar kana da isasshen space a wayar ka, sai ka kashe wayar ka kunna, idan hakan bai yi aiki ba, ka goge virtual machine ka sake sabon installing, idan duk da haka bai yi maka aiki ba, ka saurari sabon update na Application din daga playstore.

  • Me za kuyi idan aka samu matsalar network a Virtual Android?

Ku gwada canza DNS zuwa address din ku na babbar wayar ku, kamar 8.8.8.8, a cikin advance settings. Hakan yana iya magance wasu matsaloli na network

Domim Downloading na Application din Virtual Android, Danna wannan rubutun na ƙasa 👇

Abdulfatah

CEO FOUNDER OF AREWA DAILY TRICKS I'm a real YouTuber | Blogger | Programmer | Web Designer | App Developer | Crypto Trader | Cyber Army | Graphic Designer | --But sometimes I'm 🎭ANONYMOUS🎭

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button