ANDROIDAPPLICATIONS

Top 10 Android Virtual Machines, use another Android in Android

Menene Android Virtual Machine??

Android Virtual Machine (VM) manhaja ce ta software da ke bada damar amfani da wayar Android a cikin wata wayar ta Android

Da Android Virtual Machine, zaka iya amfani da wayoyin Android da yawa a cikin wayar ka guda 1, tare da samun wasu muhimman ayyuka na musamman wadanda ba’a baka damar kayi su da babbar wayar ka ba, ko kuma yin su zai iya kawo maka tangarɗa a cikin babbar wayar ka, wasu daga cikin wadannan ayyukan sun haɗa da:

 • ROOT ACCESS: kamar yadda muka sani, rooting abu ne mai matukar muhimmanci a wayar Android, amfanin sa ba zai lissafu ba, amma a takaice, zaka iya yi wa wayar ka ta virtual machine rooting cikin sauki, idan kayi rooting din wayar ka, to ka dawo da saitukan Kamfanin wayar a hannun ka, duk wani abu da kasan kamfanin wayar ne suka tsara shi, zaka iya mayar da shi naka, misali
  1. VERSION: zaka iya canza version na wayar ka idan kayi mata rooting, idan tana V9 zaka iya mayar da ita V10 ko V11 ko kuma duk yadda kake so.
  2. MODEL: zaka iya canza sunan wayar ka zuwa yadda kake so idan kayi mata rooting, kamar daga Infinix zuwa Tecno ko Itel zuwa Gionee, kokuma duk yadda kaga dama.
  3. SHOOT & BOOT: a lokacin da ka kunna ko ka kashe wayar ka, akwai abin da take nuna wa, mafi yawa sunan kamfanin wayar ne, ta hanyar rooting za ka iya canza shi zuwa duk yadda kake so.
  4. RAM: Babu bukatar sai nayi bayanin menene RAM (random access memory) da amfanin shi, ta hanyar rooting za ka iya canza RAM na wayar ka, kamar daga 2GB zuwa 3GB ko 4GB (Akwai iyaka).
  5. ROM: (Read Only Memory) Shine girman memory na wayar ka, wanda kake ajiye abubuwa a ciki, ta hanyar rooting za ka iya canza girman memory na wayar ka, kamar daga 16GB zuwa 32GB ko 32GB zuwa 64GB (Akwai iyaka)
  6. ABIN LURA: domin sanin amfanin rooting, yadda ake rooting, ko yadda za ka canza bayanan wayar da aka yi rooting, ka danna NAN
 • IMEI NUMBER: (International Mobile Equipment Identity) kowacce waya tana da nata IMEI NUMBER din (ya danganci adadin layikan da ake sanya mata), da shi ne wasu kamfanoni suke gane wayar ka a lokacin da kayi register da su, amma wayar ka ta virtual machine, za ka iya canza mata IMEI NUMBER cikin sauki, a duk lokacin da kaso.
 • DEVICE ID: Shima kamar IMEI yake, amma kuma akwai banbanci, domin kowacce waya nata daban! Shima wasu kamfanoni kan yi amfani dashi domin gane waya a wasu guraren, saidai za ka iya canza na wayar ka ta virtual machine cikin sauki.
 • IP ADDRESS: (internet protocol address) shi ke nuna daga wajan da kake hawa yanar gizo, shima ana canza na wayar virtual machine cikin sauki.
 • STORAGE: Za ka samu memoryn da zaka ajiye kayan ka a ciki (Files) na wayar virtual machine.
 • CLONE: A yanar gizo, duk wayar da kake da ita ta virtual machine, kamar ka siya Sabuwar waya ne kawai, domin komai nata ya babanta da na wayar ka.

Wannan wasu ne daga amfanin Android Virtual Machine, za ka iya fadada bincike domin sanin wasu abubuwan!

WANNE KALAR VIRTUAL MACHINE AKE SAMU?

Kowacce wayar Android, za’a iya samun virtual Machine din ta, musamman ma a hannun kamfani, saidai ba kowanne kamfani ke yarda da hakan ba saboda wasu dalilai, kasancewar idan ka same shi, babu tabbacin ka siya ita wayar, misali, kana da INFINIX HOT10, sannan kana ra’ayin INFINIX HOT9, amma baka da kudin siya, kokuma ba za ka iya haɗa guda 2 a tare ba, kawai sai ka samu virtual machine na INFINIX HOT9, ba na tunanin za ka goge shi ka je ka siya HOT9 ta ainihi 😋

Hakan yake sa mafi yawan manyan kamfanoni ba’a samun virtual machine na wayoyin da suke yi, amma duk da haka, developers na iya bakin kokarin su dan ganin cewa sun samo shi!

ME KAKE BUKATA DOMIN SAMUN ANDROID VIRTUAL MACHINE?

Ya danganci wayar da kake so, da kuma wayar da kake da ita, amma ka tabbatar wayar da kake da ita, ta fi wayar da kake neman virtual machine din ta komai, tun daga girma, version, ram, ROM, da sauran su, NB: amfani da virtual machine wanda ya fi karfin wayar ka, zai iya jefa wayar ka cikin matsala!

Akwai virtual machine na online, akwai kuma na offline, bambancin su kadan ne, amma dai ya zama wajibi ka samu DATA enough, da network mai karfi, a lokacin da zaka yi downloading din kowane kalar virtual machine!!

TA YAYA ZA KA SAMU ANDROID VIRTUAL MACHINE?

Mafi yawa Applications ne, za ka iya samun shi ta hanyoyi da yawa, wasu kyauta zaka same su, wasu kuma sai ka siya, amma ka lura sosai a lokacin siya!!! (not financial advise)

A INA AKE SAMUN ANDROID VIRTUAL MACHINE??

Za ka iya samun na kyauta a playstore, amma manya manyan wayoyi saidai a gurin developers ko kamfani, ga wasu daga cikin virtual machines na kyauta da za ka iya samu 👇

FREE OFFLINE VIRTUAL MACHINES

PAID ONLINE VIRTUAL MACHINES

Wadannan wasu ne daga cikin virtual machines na wasu wayoyi da za ka iya samu, na kyauta da na kudi, ka fadada bincike domin samun wasu wayoyin!!!

Ga masu tambayoyi za ku iya rubuta mana a comment section

MUNGODE

Abdulfatah

CEO FOUNDER OF AREWA DAILY TRICKS I'm a real YouTuber | Blogger | Programmer | Web Designer | App Developer | Crypto Trader | Cyber Army | Graphic Designer | --But sometimes I'm 🎭ANONYMOUS🎭

Related Articles

23 Comments

 1. Ogah mu Kuma muna ta Kiran darasi akan website dinda ka fada zakayi Mana shiru haryanzu gaskiya ogah yakamata ayi wannan darasi na website din adomin ayanzu duk arewa wlh Babu wata channel dake koyarwa Kuma abune Mai matukar amfani da Allah ogah 🙏🏾 ataimaka ko acikin wannan azumin ne ayi Mana shi kamar yadda Naga naka yayi kyau sosae

 2. Aslm. Oga Da Allah wayata infinix s4 CE , ana iya kara mata version daga 9 zuwa 10 ko 11?Sannan kuma za a iya yi ba sai an dorata computer ba? Sannan akwai wata matsala da zata iya samu in anyi mata rooting da canza vision din?Na gode

 3. Slm an sharuwa lfy oga Abdul yakamata akawo Mana videos Dan gane da virtual machine kamar yadda kasaba kawo Mana cigaban wadansu abubuwa muhimmai saboda wannan tsarin gaskiya Yana da matu kar amfani sosai misali kayi Mana bidiyoyi da suka shafi samun kudi da dataway shareit lite da dai sau ransu
  Sabo da wannan is important to mankind

 4. Masha Allah oga Alla yabiya
  Oga mgn folax ne ban gaba Naduba setting Amma bana gani

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button